Tuesday, 14 July 2020

Yaudara a SO❤️da Mayaudariyar Zuciya❤️me azabtar da Ruhin me yin SO❤️




YAUDARA🤦: wata kalma ce wacce data Qunshi mutum ya sanya ko amfani da wata Hikima ko dabara domin a nunawa wanda akeso a yaudara cewa gaskiya ne,amma asalin lamarin Qarya ne,wata manufa ake son cimmawa👌
YAUDARA a Musulunci HARAMUN ne,saboda zai iya Haddasa cutarwa,duk me yinta ya san hakan,kuma ana yinta a kusan komai idan me yin yaso yayi,hakan yasa SO❤️ ma ya samu nasa kamashon.🤦
Yaudara a SO❤️ya kasu kashi 2 wasu sukance 3 ,(1)fara yin so❤️ da niyyar yaudara(2)yaudara a tsakiyan SO❤️ (3) yaudara a qarshen So❤️.
Amma mafi Girman yaudara shine yaudara a qarshen SO❤️🤦sauran kuma riskar mutum suke.
Idan mutum ya tsinci kansa ya kasa tsayawa wuri ɗaya a So❤️yana yawan samun ɗimuwa har abin ya dinga damunsa wani lokacin❤️ba son ransa bane,zuciyarsa tana ta hilatarsa,yaji duk wanda ya riska da abin da zuciyarsa ke nema sai yaji SO❤️ya motsa masa a zuciya❤️,wannan shi ake kira Mayaudariyar Zuciya❤️me wahalar da Ruhin me yin SO❤️✍️
Zanci gaba da sababin rukunnan Yaudara dana lissafa yanda suke faruwa in shaa Allah.✍️✍️✍️



No comments:

Post a Comment