Sunday, 12 July 2020

Ƴan Mata zaki shige Ransa cikin Yardar Ubangiji(Saurayi) idan kika kiyaye wannan,indai na Gari ne.....






✍️A bayan Idon sa,ko kina tare dashi,kiyi qoqari ki bawa shaiɗan Kunya,karki aikata wani abu me kama da Alfasha,kiyi wa kanki wannan Alfarmar da Gatan,idan a bayan Idon sane kuma Allah bazai baki Nasara akansa ba,indai shi na Gari ne sosai,idan hakan bata faru ba,akwai yuyuwar wani abu mara dadi ya ziyarci kunnuwan sa game dake,sai kin kula.
✍️Ana Nafila don Dauwamar da SO da Qauna a zuciyar Namiji musamman Nagartacce,,kin samu na Gari,dage da faɗawa Allah,duk abin da kike so zai Miki indai baki da Niyyar cutarwa,kuma kina da Iymanin zai Miki.
✍️Taya shi Bautawa Allah,taimaka masa cikin Addininsa,haka kawai idan kika ga zai kauce kiyi masa Nasiha,ba Gatsar yanda yaran mata ke yi ba,ba daɗin ji balle a karɓa,cikin Mutunci raha da Girmamawa,dinga bashi Shawara sosai.

✍️Ki mayar da komai nashi tamkar naki,zaiji daɗi,karki dinga jingina masa shi kaɗai,zai san ana tare.
✍️Karki nuna kwadayinki a fili don yana da wani abin Duniya,bashi Shawara ,kiyi masa Tamkar ƴar Uwa ta kusa.
✍️ki zama Maqura wurin tsafta,ki dinga shiga ta Mutunci,rage chaɓa Wasu Abubuwa yayin Fita,Na gari zai dinga jin kishi sosai.

Kaɗan kenan ........koda baya tare dake zai dinga gamuwa da banbanci kala kala,kowacce gaɓa idan yaga banbanci sai yaji a ransa "Wance ba haka take min ba" ba abin dazai dinga zuwar masa a Rai sai Kewa,kinga Nasara ta samu🤝🤝🤝

No comments:

Post a Comment