Hukumar yan sandan Najeriya ta alanta niyyar daukan sabbin jam'ian yan sanda 'kurata' kuma ta yi bayanin yadda masu sha'awa zasu iya nema da sharrudan da za'a cika.
Kakakin hukumar, DCP Frank Uba, ya bayyana haka a jawabin da ya saki ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2020.
Za'a fara rijistan daga ranar 14 ga Yuli zuwa 23 ga Agusta, 2020 kuma za'ayi rijista a adireshin yanar gizo www.policerecruitment.gov.ng
Hukumar yan sanda za tayi sabon dauka, ta gindaya sharruda 14 ga masu nema Source: Facebook Ga jerin sharrudan da aka gindaya ga masu nema:
1. Wajibi ne ka kasance haifaffen dan Najeriya kuma kana da lambar katin zama dan kasa
2. Wajibi ne ka kasance mai Credit akalla 5 a jarrabawar WAED, NECO, GCE da NABTEB tare da Lissafi da Turanci
3. Kada kayi kasa da shekaru 17 da haihuwa kuma kada kafi shekaru 25
4. Kada tsayinka ya yi kasa da 1.67cm ga maza kuma 1.64cm ga mata
5. Kada fadin kirjinka yayi kasa da inchi 34
6. Ban da mata masu juna biyu
7. Kada ka kasance mai kashi a gindi ta rashawa
8. Kada ka kasance mai nakasa a harshe, kurma da bebe
9. Kada ka kasance mai gaucaccen haba
10. Kada ka kasance mai budadden kafa
11. Kada ka kasance mai lankwashasshen kafa
12. Kada ka kasance mai nakasa a hannu
13. Kada ka kasance mai ciwon ido, ko mai ido daya
14. Kada ya kasance an taba yanke maka wani sashen jiki
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
YOUTUBE
No comments:
Post a Comment