Sunday, 12 July 2020

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Ciki aikin Police?

Ina matasan da suke son shiga aikin Police? in sha Allah ranar Talata mai zuwa 14-07-2020 za'a bude website din hukumar domin shiga Nigeria Police Force "NPF".
Ga ka'idojin da sai an cika a shiga:
Dole sai kana da shaidan haihuwa na zama 'dan Nigeria, kuma kana da nambar rijistan katin 'dan kasa (NIN)
-Sai wanda yake da credit biyar na jarrabawan kammala karatun sakandare wanda akwai English da Mathematics aciki.
- Sai wanda ya kai shekaru 17 sannan bai wuce shekaru 25 ba.
.
- Sai wanda yake da cikakken hankali da lafiya, ga maza wanda tsayinsa ya kai 1.67m, ga mata 1.64m
-Sannan sai wanda fadin kirjinsa ya kai 86cm (34 inches) ga maza kadai
-Ga mata wacce take dauke da juna biyu ba zata samu shiga ba.
Wadanda suke da matsala na gani da ji, da sarkafewar hakora, baudewar kafa ko wata lalura kada su cika, kuma ba'a taba kamaka da wani laifi ba, sannan baka shaye-shaye, don idan kaje wajen tantancewa suna ganin alamar kana shaye-shaye zasu koreka.
.
Ga wadanda sukayi applying suka cika wadannan ka'idoji za'a kirasu tantancewa ranar 24-8-2020 wanda za'a kammala ranar 30-8-2020 a dukkan jihohin Nigeria da babban birnin tarayya Abuja, ga wadanda suka samu nasara za'a bayyana sunayensu a jaridun kasa da sauran kafofin yada labarai ranar 14-9-2020 inda za'a turasu sansanin horar da aikin 'dan sanda.
.
Wannan shine shafin yanar gizo wanda za'a shiga a cike form din:
www.policerecruitment.gov.ng
Kafin ka cika form din ka tabbata ka mallaki email adress mai kyau, kuma lambar shaidar 'dan kasar ka wato "NIN" mai kyau ne, kuma dai dai ne.
Rundinar 'yan sanda tana sanar da al'umma cewa wannan tsarin kyauta ne, a gujewa fadawa tarkon 'yan damfara, masu korafi zasu aika sakon su ta nan:
08100004507 .
.
e-training@recruitment.gov.ng
support@policerecruitment.gov.ng
Sanarwa daga kakakin rundinar 'yan sandan Nigeria na kasa.

No comments:

Post a Comment