Sunday, 12 July 2020

Labaran Safiyar Lahadi 12/07/2020CE - 20/11/1441AH. Cikakkun labaran



An sami karin mutane 664 wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya jimilla 31,987.

Kudaden da jama'a ke hadada da su sun ragu a watan Yuni zuwa Naira Trilyan 2.29.

Gwamnatin jihar Gombe za ta shuka sama da bishiyoyi miliyan 1 a 2020.

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga da dama a kauyen Arufu da ke jihar Taraba.

Fyade: Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umurnin duk masu kangon gini su gida ko kuma a daure su.

Dakataccen mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu ya ce zargin da ake masa ana yunkurin bata masa suna ne.

Gwamnatin Mali na neman yin sulhu da masu zanga-zanga.

Shahararren dan wasan fim din Indiya Amitabh Bachchan ya kamu da cutar Coronavirus.

Majalisar Mujami'un duniya ta caccaki Erdogan na Turkiyya kan maida Hagia Sophia Masallaci.

Musulmi na alhinin cika shekaru 25 da yi musu kisan kare dangi a Bosnia.

No comments:

Post a Comment