Dalilai 6 marasa ma'ana da yake HURA wutar KISHI a Zuciyar ƴaƴa Mata 🧕🧕🧕Lokacin da Miji yace zai qara Aure,kusan dukkan mata suna jin 1 daga cikin 6 nan.....
✍️Tana ji har cikin Zuciyarta ta yaya za ta fara raba Mijinta da wata Macen(Sharing) idan ta fara wannan tunanin sai Qwalla ta cika Idonta,kukan zuci,wata ma har sai ta yi Hawaye.
✍️Zata fara Nazarin,ina son yamin abu kaza da kaza duk bai min ba,yanzu idan ya qaro wata ta yaya zai min? Ko kuma yanzu duk abin da nake SO itama sai an mata kenan ban isa na samu Gatan Kaɗaitaka ba?.
✍️Yanzu idan yaje ya Auro min ƴar Gidan mushrikai fa,tazo tamin wani Asirin ko tayi wa mijina,gashi Ni ban iya bin Bokaye ko ƴan tsibbu ko ƴan Duba ba,ko kuma ya Auro ƴar Jaraba tazo ta hana musu duk wani Farinciki na cikin Gida.
✍️Yanzu kenan yanda yake min Murmushi haka zai dinga mata? Yanda zai faranta min ya min soyayya itama duk haka zai dinga mata blah blah,sai ta fashe da kuka wata.
✍️Idan muguwa ce sai ta fara tunanin Yanzu itama zuwa za tayi ta haihu dashi? Kenan Gadon sama har da nata ƴaƴan,gaskiya bana son ace yana da wasu ƴaƴan sai nawa kaɗai.
✍️ko tace Ni bani da wani dalili,wallahi kawai na tsani naga wata macen kusa da Mijina,sai naji kamar zan mutu don Kishi,bazan iya Jura ba gwanda nabar masa Gidansa naje na auri wanda bana So,ko ya kula wata ba damuwa.
Albishir ga duk wacce tayi Haquri da zafin kishi da zugar shaiɗan gami da Saqar zuciya shine..."Lada irin na Wanda yayi Jihadi.
Allah shi kyauta.Ameen.
#Aunty_zuhra✍️
اللهم جدد الايمان في قلوبنا
ReplyDeleteAllahumma jad-didil imana fi qulubina