Sanarwar da me magana da yawun ‘yansandan, Frank Mba ya fitar na cewa, akwai guraben aikin ‘yansandan 40,000 da wanda za’a dauka zasu cike.
1) Saidai dole mutum ya zamana yana da lambar zama dan kasa ta NIN
2) Sannan yana da 5 credits a jarabawar kammala sakandare.
3) Sannan yana tsakanin shekaru 17 zuwa 25.
4) Sauran sharudan sune, Mace kada ta gaza tsawon 1.64m, Namiji kuma kada ya gaza tsawon 1.67m
5) Namiji dole ya zama yana da fadin kirji na akalla inci 34.
6) Ba za’a dauki mace me ciki ba.
7) Duk wanda yasan ya taba yin wani abin kunya ko kuma ana binshi bashi ba za’a daukeshi ba.
8) Ba za’a dauki me in ina ba.
9) Wanda hakora ko habarshi ta lalace ba za’a daukeshi aikin ba.
10) Wanda gwiwoyin kafarshi ke kallon juna ba za’a daukeshi aikin ba.
11) Wanda ke da kafafu gwami, ba za’a daukeshu aikin ba.
12) Wanda kafarshi bata tsaye kyam shima ba za’a daukeshi aikin ba.
13) Wanda hannunshi baya aiki da kyau ba za’a daukeshi aikin ba.
14) Wanda baya gani da kyau ba za’a daukeshi aikin ba.
15) Duk wanda aka cirewa wani bangare na jiki ba za’a daukeshi aikin ba.
KANUN LABARAI
No comments:
Post a Comment