Saturday, 11 July 2020

Hanya Mafi sauqi da Mace Budurwa zata gane Namiji da Gasken gaske yana Sonta

Hanya Mafi sauqi da Mace Budurwa zata gane Namiji da Gasken gaske yana Sonta,ko yayi Basaja ta wani ɓangaren gaskiya ta wani ɓangaren bazai shaa ba...........
✍️Ki lura! da yanda yake baki kulawa koda da wasa ne kikace masa "Baki da lafiya" .
✍️Ki lura! bazai dinga manta kalmomin ki ba.
✍️Ki lura! Babu zancen Gajiyawa dake,Farincikin sama shine Kasantuwarki kusa dashi.
✍️Ki lura! Cikin kalmominsa dole gaskiya tafi yawa.
✍️Ki lura zai damu da Damuwarki da Farinciki da farincikinki,kuma zaki ga yana son kowa da komai naki.
✍️Ki lura baya son idan kina son yin magana yaga kin fasa,zumuɗi yake game da kalmominki.
✍️Ki lura zaki ga yana baki lokacinsa sosai,wasu lokutan yana Busy sosai amma baya iya tsallake ki koda babu yawa ,kuma zai faɗa miki uzirinsa saboda tsoro yake karki ji wani susa na wani damuwa arai.
✍️Idan son yayi nisa sosai a zuciyarsa,lokuta da dama ba sai kinyi magana ba,zai dinga fahimtar Motsin zuciyarki,idan kina cikin damuwa koda kin ɓoye sai ya gane,koda zancen Raha kike masa,haka idan kina farinciki.
Akwai Alamomi da dama ,wannan wasu ɓangare ne.
Allah ya haɗa ƴan mata da samarinmu da Masoya na gaskiya.Ameen.

No comments:

Post a Comment