Friday, 10 July 2020

AN KAMA MASU SHIGO DA KAYAN TA'ADDANCI NIGERIA

Alhamdulillah jami'an tsaron Kasar jamhuriyar Nijer (GENDARME) sun samu nasaran kama wasu matasa guda biyu da manyan makamai na ta'addanci suna kokarin shigo dasu Nigeria ta yankin jihar Sokoto

An samu bindiga kirar AK47 guda 21, da harsashin bindiga kirar AK47 sama da dubu biyu a tare da su zasu kai jihar Sokoto

Bayanan sirri ya nuna ana safaran muggun makamai daga jamhuriyar Nijer ana kaiwa 'yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso yamma ba, Alhamdulillah an fara kamasu

Muna rokon Allah Ya ciga da tona asirin masu safaran makamai, Ya kare mu daga sharrin su Amin

No comments:

Post a Comment