Saturday, 11 July 2020

Wasu daga Alamar da Namiji zai gane Mace tana sonshi da Gasken Gaske(1).


Mata Kala kala ne,yanda wata take nata takun da Salon ba kamar na wata ba,sai dai zan kawo  kaloli mafi Rinjaye,wato Kala 3.

Mace ta Farko itace MISKILA.

 Ita wata iriyar Macece wacce take jin Kanta Tamkar wata Sarauniya,da SO yana Kisa sai dai a ɗauki Gawarta domin baza tace tana yin SO ba,amma kuma idan akace ana Sonta akan iya samun Soyayyar ta,sai dai zama da ita yana da ɗaci ga wanda bai san yanda zai bi da ita ba,amma idan aka samu Soyayyarta kuma tana yi da gasken gaske a lura da abu kamar haka....

✍️Tana da tsananin Kishi! bata son ka kula kowacce Mace sai ita,saboda tana jin ta Isa! Kuma idan aka kula wata Qasqanci ne gareta,to zata dinga nuna kishi maqura ,amma Kishi me Aji wanda zata iya Rabuwa da Wanda take SO gaba ɗaya ma,ba tare data faɗa mish dalili ba a wasu lokutan koda Son zai kashe ta,nuna damuwarta kan ka kula wata shine Alamar tana Sonka,idan bata So bata Qorafi ko zaka kula mata 1000.

✍️A lura za tayi fushi na sosai idan ba'a nuna mata damuwa sosai,koda ita bata nunawa,alamar tana yin Son shine Qorafin da zata buɗe baki tayi,idan bata yin So zata manta ma baka neme taba kaji yanda take ba,ko wuni akayi ba'a kira taba za tayi fushi sosai,kuma bai zama lallai idan ka kira ta ɗaga ba,koda Hawayenta ya zuba kan bata ji ka neme taba,zuwanka ka rarrashe ta sosai shine yake sauqar da fishinta,wannan Damuwar da tayi shine SON.

✍️Tana da tsananin Jan aji,amma kuma me matuqar sauqin kai ga wanda ya iya zama da ita,Alamar tana yin SO shine ko da yaushe so take ka damu da ita kuma ka SO ta, Ita wata iriyar Macece wacce da wuya ta iya haɗa maza 2 ta sosu,sai dai bata ɗaukan Wulaqanci ko kaɗan,zata bayar da SO idan an bata,zata kyautata idan an kyautata mata,sannan zata jajijrce idan an jajirce akanta.

Ita dai wannan baiwar Allah ,haka take nata kalan SON,Miskilar mace kenan,wacce SO yafi yiwa bulala amma sai an qure take bayyana shi✍️

Allah shi kyauta.Ameen.

Zanci gaba In shaa Allah ✍️✍️✍️

#Aunty_Zuhra✍️

No comments:

Post a Comment