Sunday, 5 July 2020

menene hukuncin Mutumin da har ya tsufa bai tabao zuwa Sokoto ba?

MAI TAMBAYA YANA CEWA...

"Malama wai menene hukuncin Mutumin Gombe, Adamawa, Borno, Kaduna, Kano, Niger, Zamfara, Kebbi, Katsina ko dan Bauchi da har ya tsufa bai tabao zuwa Sokoto ba? 🤔"

MALAM yace 😳. Toh! a Kauli mafi rinjaye dai sun tafi akan cewa zuwa garin Sokoto rabo ne, sai wanda ke da rabo zai sami damar zuwa.

Amma a wani qaulin, lallai duk wanda yake lafiya kalau, har ya tsufa bai ta6a zuwa Sokoto ba, to lallai ya tafka babbar asara.

SAIDAI KUMA..... A wata ruwayar tazo da sassaucin cewa, idan ka taba gaisawa da dan Sokoto ko a chatting ne, ko ka gaisa da wanda ya ta6a zuwa Sokoto 🤝🏻 to da dan sauqi.

Muna fatan Allah ya baiwa wadanda basuje ba damar zuwa Sokoto.
Amin summa Amin 🙏🙏🙏🙏
🤣🤣🤣🤣

No comments:

Post a Comment