Tuesday, 7 July 2020

Shawara Guda 4 Yan Mata! Idan Kikayi Amfani da ita Zaki Gode wata Rana.

(1)Kiyi Haquri da abin da Iyayenki suke miki ko suke Baki na Hidima,duk Talaucin su,idan ta qure ne! ki nemi sana'a kiyi ko ki koya wacce babu zubar da Mutunci a cikinta.
(2) Kiyi haquri duk irin kayan da zaki ga Qawa ta saya ta saka,wanda kika san Iyayenki ko sana'ar da kike baza ta iya yi Miki su ba,ki kawar dakai daga kansu,ko Yawon Biki da anan ake jelen Gulmar kin saka ko baki saka ba,ba dole ne sai kinje ba ,zaki iya zuwa kafin Biki ko bayan Biki kiyi musu murna da Addu'a.
(3)Ahir! Ɗinki da cewa Namiji yayi Miki abu kaza da kaza,ko da ya matsa miki kan yana son ya Miki ki kasance me aji kafin ki karɓa,kar kuma ki bari wata kyautatawa da yake Miki tasa ki chanja daga yanda kike mu'amalantarsa,kamar misali don ya Miki Hidimar 10k ki fara washe masa baki,wannan Zubar da Qimar ki kike,idan bakya washewa ki zauna a hakan ki,karki sauya don ya baki wani abu,ko da kyautar sa ko ba kyautarsa ki zama kina nan yanda kike mu'amalantarsa,saboda idan kika zamo me araha don abin Duniya,cikin sauqi za'a saye ki da abin Duniya,kuma zai gane cewar sai yana miki kyauta yake samun kanki,in babu kyauta ba ki da sauqin kai,kinga kin faɗi wanwar! KI KULA!

(4)Duk rintsi Namiji yazo Gidanku ya same ki,idan yana son magana dake ko son ganin ki yazo Gidanku,koma dai menene yazo Gidan ku!!!!!!!!🤔

No comments:

Post a Comment