Sunday, 5 July 2020

Soyayya da Ustaziya Original



....
Wato Soyayya da Ustaziya Original akwai wahala,saboda ita soyayya da ita ba kamar Soyayya da ƴan mata gama gari bane👌🤗

Ƴan Mata Gama gari zaka iya zuwa ka tsara su,har ka samu su shiga,su dinga washe maka Baki,toh ita kuma lamarin Ustaziya Original ba haka lamarin yake ba🤗

Kana Fara magana kamar kana magana da Lauya ne,idan baka iya Allonka ba a bugu ɗaya zata ɓaro ka🤗karka ce zaka dinga mata hirar abubuwan Qyalqyalin Duniya,ko Zancen kana da abin Duniya,tunda dai ka san ita ba binka za tayi kuje shaqatawa ba,indai ba Aurenta kayi ba.

Ustaziya ba abin dake Kama zuciyarta sai Gaskiyarka👌Tsoron Allahn ka👌kyawun Halinka,da kuma sonka da Addini,sai kuma iya soyayya da kuma Qwarewa wurin bayar da kulawa a aikace,da sauran Ɗabi'u masu kyau,bana tunanin bayan wannan Ustaziya Original zata so ka don shi.

Soyayya da Ustaziya sai anyi taka tsantsan na sosai,saboda Abu kaɗan zai iya rikita tunaninta,ba komai bane face ,ta samu wani hali Mummuna a tare dakai,idan tafiya tayi tafiya,sai taji baza ta iya kasancewa dakai ba kuma tunda bata Aure kaba,gaba ɗaya Tanadinta tafi son Namijin dazai nuna mata hanyar Allah ko yaushe,wanda zai kula da ita,ya kula da ƴaƴanta,bayan hakan bata neman komai👌👌👌

Na lura Ustaziya tana yin SO me tsafta idan ta samu wuri,kuma tana yin SO me qarfi sosai,sai dai bata Son Namiji daba irinta ba,duk Namijin daba irinta ba,da wuya taso shi sai in Qaddara,sai dai ta masa kara.

Allah yasa mu gama da Duniya lafiya .Ameen.

#Aunty_zuhra.

No comments:

Post a Comment