Thursday, 2 July 2020

Duniyar Masoya: Yanayin Zuciyar Namiji Game da SO



Kwanaki munyi magana akan yanayin Zuciyar❤️ ƴa Mace🧕game da SO❤️...
Toh ta fannin Namiji🧔 shi kuma abin ba haka bane👌

Namiji🧔sau da yawan lokuta yana yin SO❤️ne kan wasu dalilai ko dalili,sai dai babbar Illar zuciyar Namiji shine idan waɗannan dalilin suka samu mishkila yana iya sawa ya daina SO❤️ko ya rage sosai👌
Mu kanga dare ɗaya Namiji ya nace akan SO❤️harma a dinga masa kallon mara zuciya,sam ba haka bane,katari yayi da muradinsa,wannan abin shi yake ingiza shi kan jajircewa,wanda kuma wataqila ita kanta wacce ya nacewan bata san dalilin ba👌da Qaddara zata sa dalilan nan su gushe a hankali shima zai fara ja da baya,ko kuma ya kau da hankalinsa daga kan wannan SON❤️.
Misali: Wani Burinsa shine ya samu Mace me kunya,Biyayya,da kuma Kamewa daga Alfasha,toh kwatsam kamar yanda suka saba halin nasu,sai ya fara tirzawa har yakai ga cikar tabbacin ya samu abin da yake nema,to fa shi yaga wurin zama,indai har tabbacinsa ya kai tabbaci,toh amma da ace yarinyar zata bar duk waɗannan ɗabi'un zai iya dakatawa yaga inane matsalar idan yaga da gaske take tofa zai iya zubar da wannan SON❤️,harma ya dinga Asha ruwan tsintsaye a wasu lokutan.
Shi yasa akace Dalili ke riqe Namiji a SO ❤️ har ya tsaya ya jajirce akansa,gami dayi masa Hidima,ya nuna haquri da juriya a cikinsa,idan aka samu akasin hakan to akwai Lauje cikin naɗi a lamarin,iya nutsuwar namiji a cikin SO❤️iya Hidimarsa da jajircewarsa a cikinsa,wani zai iya tara mata 10,amma akwai wacce ya daraja matuqa a cikinsu,saboda itace muradinsa yafi Nutsuwa da ita.
Allah ya haɗa kan Masoya.Ameen.

No comments:

Post a Comment