Thursday, 2 July 2020

Abubuwa (5) ne zai sa kiga ya janye maganar Aurenki,ko ya daina zuwa gidanku Bayan anyi maganar Aure dashi


Abubuwa (5) ne zai sa kiga ya janye maganar Aurenki,ko ya daina zuwa gidanku Bayan anyi maganar Aure dashi ko ya fara wasa....
1)Allah bai qaddara zaki Aure saba.
2)matsalar Jinnu.
3)Tarbiyyarki ko ta gidanku bata masa ba bayan yayi bincike.
4)Ruwan Ido da wasiwasi saboda ya hango wata wacce ta fiki,dama kawai zai Aureki ne saboda ya rasa irin wacce yake so sai kuma ya gamu da ita,ko kuma yaji kamar zaiyi kuskure idan ya Aureki.
5)Dama ba Auren ne ya kawosa ba, so yake ya baza Haja idan tayi ruwa rijiya idan bata yi ba qasa,sai kiga ya gudu kin daina ganinsa ko ciniki ya faɗa ko bai samu sa'a ya faɗa ba.
Idan hakan ta faru dake kice "Allah yasa haka shi yafi alkhairi,Allah ka zaɓa min mafi alkhairinsa" idan kika yi hakan kin hutashshe dakanki doguwar damuwa da qwarzababben tunani.Allah ya zaɓawa 'yan matanmu mazaje na qwarai,Ameen.

No comments:

Post a Comment