Tuesday, 30 March 2021

Matar da Namiji yake Son Aura indai ya san abin da yake yi......



Matar da Namiji yake Son Aura indai ya san abin da yake yi......

✍️_So yake ya Auri wacce idan ya shigar da ita cikin zuri'ar sa iyaye da ƴan Uwa zasu ce Gwanda da akayi.

✍️_Tunani yake wacece zata Bawa ƴaƴansa Tarbiyyar data dace?

✍️so yake ya samu wacce zata mutuntashi,ta mutunta Iyayensa,ta riqe masa Amanar Gidansa da kanta.

✍️Hasashensa Gidansa ya kasance cikin tsafta ko yaushe bayan yayi Aure.
✍️_So yake ya Auri wacce zata iya dafa masa Abinci ta sanyaya maqoshinsa idan ya dawo Gida.

✍️Fatanshi History din mace ya nuna bata bin GAYU,bayan yayi bincike da Nazari.

Ƴan Mata wannan Qalubale ne a gareku,domin kusan 80%na maza wannan👆 shine tunaninsu.

Shin....ta yaya kina Rawa kina watsawa zai kwashe ki? Tayaya kina swags kina watsawa zai kwashe ki? Ta yaya kina turo qugu kina turo Qirji kina watsawa zai kwashe ki?  Ta yaya kina Hoton fitsara kina watsawa zai kwashe ki?

Zai iya cewa kinyi kyau kanki yana Qato,zai kuma iya furta Miki "I love You" amma fa ki sani Yaseen ta Aure sai ya zaɓa,bakya cikin list,bar ganin kina da kyau,ba waɗanda zaki gani a qofar Gidanku sai yan Swags,daga Qarshe ki qare a Auren wanda bakya So,shi wanda yake Miki Qaryar yana Sonki,ya zille,yace Iyaye sunce masa "Ba yanzu zaiyi Aure ba,ko an bashi cousin sis😊🙄🙄

Allah ya gyara Halayenmu.Ameen.

#Aunty_Zuhra.

No comments:

Post a Comment