Buhari ya kai wa ‘Yan Majalisa kudirin da ake jira tun lokacin Shugaba Obasanjo
- Fadar Shugaban kasa ta kai kudirin PIB gaban Majalisar Tarayyar Najeriya
- Kusan shekaru 10 kenan ana ta jiran wannan kudiri da zai gyara harkar mai
- Idan kudirin ya zama doka, gwamnati za ta yi watsi da kamfanin man NNPC
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin PIB na shekarar 2020 a gaban ‘yan majalisar tarayya.
Rahoton ya bayyana cewa wannan kudiri zai bada damar kafa sabon kamfanin man Najeriya. A dalilin haka kuma za a yi fatali da kamfanin man NNPC.
Idan wannan kudiri ya samu karbuwa kuma har ya zama doka, gwamnati za ta soke hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya.
Wannan kudiri ya ba Ministocin kudi da na man fetur ikon ganin yadda za ayi gwanjon dukiyoyi da duk kadarorin NNPC ga sabon kamfanin da za su gaje su.
Kamar yadda jaridar ta bayyana, sashe na 54 (1, 2 da 3) ne su ka ba Ministocin kasar wannan iko.
No comments:
Post a Comment