Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, DR. Isa Ali Pantami ya karyata jita jitar da ake yadawa game da shi cewar ya mallaki wasu maka makan gidaje a birnin tarayya Abuja.
Tun da farko dai jarida ce ta wallafa cewar Ministan ya mallaki wasu maka makan gidaje guda uku a unguwar Wuse dake babban birnin tarayya Abuja ga matansa uku.
Ministan ya kara da cewar, tun da ya zama Minista bai mallaki wani gida ba na kashin kansa a ko Ina a fadin duniya. Dan haka yake kira ga mutane da su yi watsi da jita jitar da ake yadawa.
No comments:
Post a Comment