Idan Allah Ya kaimu gobe Litinin, Maigirma
shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya zai rantsar da kwamitin da za suyi aikin 'diban matasa dubu dari bakwai da saba'in da hudu (774,000) a jihohin Nigeria 36 har da Abuja
shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya zai rantsar da kwamitin da za suyi aikin 'diban matasa dubu dari bakwai da saba'in da hudu (774,000) a jihohin Nigeria 36 har da Abuja
Tsarin diban aikin zai kasance mutane dubu daya (1000) daga kowace karamar hukuma a Nigeria, wadanda zasu su dinga karban Naira dubu ashirin (20,000) duk wata a tsawon lokaci da aka tsara za suyi aikin, shirin zai fara aiki nan da watanni biyu masu zuwa, farkon watan October Insha Allah
Idan an kafa kwamitocin gobe; zasu isa jihohin su domin kafa kwamitocin kananan hukumomi, daga bisani za'a sanar da tsarin aikin da yadda mutane zasu shiga, wannan abin alheri yana zuwa ne a zangon karshe na mulkin shugaba Buhari wanda yake fatan ya rage wa matasa maza da mata radadin rashin aikinyi.
Shugaba Buhari alheri ne, bai cancani ayi masa tawaye ba balle zanga-zanga, 'yan uwa matasa mu taimaka masa da addu'ah da kuma hakuri domin ya share mana hawaye
Yaa Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Allah Ka raba tsakaninsa da maciya amana, Allah ka fitar dashi kunyar duniya da na lahira Amin
Allah ya taimaka
ReplyDelete